Boc Madaki – Wasika Zuwa Sama (+ Lyrics)Another Masterpiece by Boc Madaki titled "Wasika Zuwa Sama" See Lyrics Below. WASIKA ZUWA SAMA(Lyrics) 

CHORUS 
Mutuwa(4x) 

VERSE ONE
*Baba, Mutuwar Ka Bai Zo Mana Da Sauki Ba 
*Abun Takaicin Ma 
*Shi Ne Da Mun Wuce Mutan Anguwa Suna Hira 
*Maimakon Mun Jaje Da Tausaya Wa Yanayi Na 
*Sai Ka Ji Sun Ce Na Chacchanci Azaban Da Ke Bi Na 
*Kullum Mama Tana Cikin Tunani, Sun Ki Barin Ta Ta Huta, Suna Ta Kiran Ta Maiya 
*Ba Fada Mun Aka Yi Ba Na Ji Na Gani Da Kai Na 
*Ya Zan Yi Da Rai Na 
*Duk Da Dai Da Sanin Mu Cewa Da Kudin Ka Ka Gina 
*Baba Karami Sun Zo Sun Kore Mu Sun Sai Da Gidan
*Wai Don Mama Ba Ta Taba Haifan Yaro Na Miji Ba 
*Kuma A Al'adan Ku Ba A Raba Gado Da Iri Na 
*Sai Ka Ce Ni Na Hallaci Kai Na 'Ya Mace 
*Ashe,Rayuwar Wassu Marayu Haka Ne 
*I'm In Pain Hoping For Better Days 
*While I Pray You Are In A Better Place 

CHORUS 
Mutuwa(4x) 

VERSE TWO 
*Mama,Mutuwar Ki Ya Bar Mu Cikin Azaba 
*Ba Mu Samun Kula A Kan Kari Yadda Muka Saba 
*Barin Ma An Daina Sa Mana Abincin Mu Da Nama 
*Mun Daina Zuwa Makaranta Don Bamu Samun Dama 
*Daga Dan Gaban Goshin Ki Yanzu Ni Ne Bawar Gidan 
*An Sallami Baba Mai Aiki, Ni Ne Na Mai Da Gurbin Ta Sai Dai Ni Din Ba A Biya 
*Da Safe Ni Na Kan Riga Kowa Tashi 
*Da Dare, Kowa Ya Kan Riga Ni Barci 
*Kanne Na Duk Sun Koma Zama Da Kawu A Kauye 
*Duk A Bayan Mutuwar Ki Don Baba Ya Sake Aure 
*Mun Yi Matukar Rashi 
*Fiye Da Manomin Da Bayan Damina Mai Albarka Wuta Ya Kone Masa Hatsi 
*Oh Mutuwa! Ya Sace Mu Wane Dan Fashi 
*Da So Shi Ne Samu,Ki Dawo Rayuwa Ko Na Minti Daya In Gan Ki
*Wasika Daga Dan Ki

CHORUS 
Mutuwa(4x)

VERSE THREE 
*Da Na Makadaici 
*Mutuwar Ka Ya Faru Ne Kamar A Mafarki 
*Ko Zan Gan Ka A Raye In Na Farka Daga Barci 
*Ka Tafi Ka Bar Mutan Duniya Na Ta Mun Habaici 
*Kullum Ina Cikin Tamabaya,Shin  Ta Wani Hanya Na Yi Wa Rayuwa Laifi 
*Ji Nake Kamar Ni Ne 'Yar, Kai Ne Mahaifi 
*Da Safe In Zan Fita Wa Zai Ce Mun Sai Anjima, 
-Wa Zai Ce Mun Maraba In Na Dawo Da Maraici 
*Wa Zai Haifa Mini Jika? 
*Wai Zai Ce Mun Yana So? Wa Zai Karba In Na Mika? 
*Tunda Mahaifin Ka Ma Ba Ya Nan Wa Zai Mini Hira 
*Wai Karfafa Ni,Wa Zai Gina Mini Gida 
*Tun Ranar Da Na Haife Ka Na San Zaka Zamo Soja 
*Har Hakan Ya Zamo Gaske 
-Ka Yi Nasara A Yakin Farko,Ka Dawo... Daka Koma 
*Labarin Mutuwan Ka Ne Ya Kwankwasa Mini Kofa 
*Wish I Stopped The Bullet 
*Wish I Had Made The Trigger Disappear Before They Pull It 

CHORUS 
Mutuwa(4x)
Post a Comment

0 Comments